Gwamnatin Jahar Kano ta Fadi Yankin da ya Dace a Fitar da Shugaban Kasa a 2023
Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan Kano ya ce yana goyon bayan a mika mulki ga kudancin Nigeria a 2023.
Gwamnan ya ce duk da cewa tsarin karba-karba baya cikin kudin tsarin mulki, tsari ne da ke taimakawa a ci zabe.
Ganduje ya kuma ce yana kyautata zaton APC za ta sake cin zaben mulkin kasar a 2023 domin cigaban da aka samu a tsaro da tattalin arziki a karkashin mulkin Buhari.
Gabanin babban zaben da ke tafe a 2023, Gwamnan Jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya kamata a bawa kudancin Nigeria tikitin takarar kujerar shugaban kasa.
Ganduje ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today a Channels Television da aka haska a ranar Juma’a.
Read Also:
“Kudancin Nigeria ya dace a bawa takara amma ya kamata a samu hadin kai tsakaninsu,” ya ce a yayin da ya ke amsa tambayar game da yankin da ya dace ta fitar da shugaban kasa a 2023.
“Kudancin Nigeria ya dace a bawa takara amma ya kamata a samu hadin kai tsakaninsu,” ya ce a yayin da ya ke amsa tambayar game da yankin da ya dace ta fitar da shugaban kasa a 2023.
“Karba-karba duk da cewa bata cikin kundin tsarin mulkin jamhuriyar tarayyar Nigeria tsari ne na cin zabe.”
Da aka masa tambaya shin ko APC ta tabuka abin a zo a gani tun bayan lashe zabe da ta yi a 2015, ya amsa da cewa eh.
Ya ce jam’iyyar APC a karkashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ta inganta tsaro sannan tana gyara tattalin arzikin kasar.
Ganduje ya ce yana kyautata zaton jam’iyyar mai mulki za ta yi nasara a babban zaben 2023 da ke tafe ta cigaba da jagorancin kasar.
Amma ya ce akwai bukatar jam’iyyar ta yi shiri mai kyau tare da bincike kan hanyoyin da suka fi dacewa domin sake cin zabe a kasar.