Sokoto: ‘Yan Sanda Sunyi Nasarar Kashe Wasu Masu Garkuwa da Mutane Tare da Kama Wasu

 

An kashe wasu mutane 2 da ake zargin ‘yan fashi ne a karamar hukumar Tambuwal dake jihar Sokoto.

Sannan ‘yan sandan sun samu nasarar damkar wasu masu garkuwa da mutane guda 8.

An samu bindigogi kirar AK-47 a hannunsu, da kuma sauran miyagun makamai.

An kashe wasu mutane 2 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a wuraren Sanyinna da ke karamar hukumar Tambuwal a jihar Sokoto, yayin harbe-harbe da ‘yan sanda.

Kwamishinan ‘yan sanda, Ibrahim Sani Ka’oje ya bayyana hakan a ranar Asabar a wani taro da suka yi a hedkwatar ‘yan sanda, Channels TV ta wallafa.

Kamar yadda yayi bayani, ana zargin daya daga cikinsu da fashi da makamai a sati 2 da suka wuce, inda ya kashe mutane 2 a wuraren Tamaje da ke jihar, amma an damke shi.

Fashi 4 da aka yi, wanda aka kama mutane 8 da ake zargin ‘yan fashi ne da miyagun makamai. Garin hakan ne aka amshi AK-47 da sauran miyagun makamai daga hannunsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here