‘Yan Ta’adda Sun Kai Hari Mainok Dake Jahar Borno Sun Kona Ofishin ‘Yan Sanda
‘Yan Boko Haram sun sake kai hari jahar Borno, in da suka kona ofishin ‘yan sanda a Mainok.
Mazauna yankin sun bayyana cewa, da yawansu sun tsere zuwa daji don tsira da rayukansu.
Mazaunan sun kuma bayyana cewa, sojojin saman Najeriya sun kawo dauki inda suka fatattaki ‘yan ta’addan.
Wasu da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne sun kona ofishin ‘yan sanda na Mainok a ranar Lahadi sakamakon mamayar da maharan suka yi wa sansanin sojoji kafin sojojin Najeriya su fatattake su.
Read Also:
Da yake tabbatar da hakan ga jaridar Leadership, Hakimin Kauyen Mainok, Lawan Tuja Mainok, ya ce ‘yan ta’addan sun mamaye sansanin sojoji da motocin bindigogi shida da misalin karfe 1 na rana kuma suka yi wa sojojin barna.
Hakimin kauyen ya kara da cewa a daidai lokacin da ‘yan ta’addan suka shigo da motocinsu na bindiga, suna harbin iska, wanda hakan ya tilasta mazauna tserewa zuwa gidajensu, yayin da wasu suka gudu zuwa dajin da ke kewaye.
Ya ce bayan kimanin sa’a guda suna harbe-harbe, da isowar jirgin yakin sojojin saman Najeriya, ‘yan ta’addan sun tsere daga yankin don haka harbe-harben ya tsaya.
”‘Yan ta’addan sun zo ne da misalin karfe 1 na rana tare da motocin bindigogi kimanin shida a gaban idanun mu suka shiga cikin sansanin sojoji.
“Sojojin da ke wajen sun yi artabu da ‘yan ta’addan kuma karar harbe-harbe ya tursasa mu zuwa gidajennmu, yayin da wasu suka gudu zuwa cikin dajin da ke kusa da su don tsira.