Zaɓe na Tafiya Yadda ya Kamata a Edo – Ɗan takarar APC

 

Dan takarar jam’iyyar APC mai hamayya a zaɓen gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya ce ya yaba da yadda tsarin zaɓen gwaman jihar ke tafiya.

Yayain da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan kaɗa ƙuri’arsa, Mista Okpebholo ya ce hukumar za ben ƙasar INEC ta yi abin da ya kamata wajen shirya zaɓen kuma komai na tafiya yadda ya kamata.

”zaɓe sai godiya, ana dab da ceto jihar Edo, hukumar INEC ta yi ƙoƙari matuƙa wajen shirya wa zaɓen nan, kawo yanzu dai ba mu ga wata matsala ba”, in ji shi.

Ya ƙara da cewa magoya bayansa na cikin murna fa farin ciki, kasancewa sabuwar Edo na dab da tabbata.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here