A Shirye Nake na Tattauna Kai Tsaye da Shugaban Rasha – Zelensky
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce duk wata tattaunawa da za a yi kan makomar ƙasarsa, wajibi ne a sanya ƙasashen yamma da Amurka da Rasha da kuma Ukraine din a ciki.
Read Also:
A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, Volodymyr Zelensky ya ce a shirye yake ya tattauna kai tsaye da shugaba Vladimir Putin, idan har hakan ne zai kawo ƙarshen yaƙin da suka kwashe kusan shekara uku suna gwabzawa.
Sai dai shugaba Zelensky ya sake nanata buƙatarsa ta ƙarin makamai domin ci gaba da samun nasara kan Rashar.