Abubuwan da Zan yi in na Zama Shugaban Kasa – Bukola Saraki

Kauna – Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa idan yan Najeriya suka zabesa, zai kawo karshen matsalar tsaro, yunwa, da rashin aikin yi.

Saraki, wanda dan takara ne karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), yace a mtsayinsa na Likita, ba dan Najeriyan da zai sake biyan kudin jinya a asibiti.

Ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai wa deleget din jam’iyyar PDP a jihar Kaduna, rahoton The Nation.

Yace:

“Idan na zama shugaban kasa, zan magance matsalar rashin tsaro. Zan farfado da masaka da kamfanonin mai. Kuna bukatar mutumin da ake ganin girmansa a gida da waje.”

“A matsayina na Likita, zan tabbatar da cewa babu wanda ya sake biyan kudin asibiti. Wannan zai yiwu kuma zamuyi Insha Allah.”

A Kaduna, Saraki ya ziyarci tsohon gwamnan jihar, Sanata Ahmad Makarfi, da tsohon mataimakin shugaban kasa, Mohammed Namadi Sambo, don neman goyon bayansu.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here