Malamin Addini yayi Addu’a kan ALLAH ya Hada Shugaba Buhari, El-Rufai da Garba Shehu da ‘Yan Ta’adda

 

Fitaccen malamin addinin Islama ya caccaki gwamnatin Buhari da mukarraban shugaban kasa.

Bello Yabo ya koka da yadda ‘yan Najeriya ke ciki saboda gazawar gwamnati wajen magance matsalar tsaro.

A makon da ya gabata ne aka ga wani bidiyon dake nuna lokacin da ‘yan bindiga ke barazanar sace shugaban kasa Buhari.

Najeriya – Shahararren malamin addinin musuluncin nan na Sokoto, Bello Yabo, yayi addu’ar Allah ya hada shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu da ‘yan ta’adda.

Addu’ar Bello Yabo na zuwa ne kwanaki kadan bayan fitowar wani bidiyo da ya nuna lokacin da ‘yan bindiga ke zabgawa wasu da suka sace bulali tare da yin barazanar sace Buhari da El-Rufai.

Garba Shehu ya bayyana martaninsa da ganin bidiyon lakadar fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna, inda ya ce ba komai bane face yada farfaganda.

A kalamansa:

“Aikin ‘yan ta’adda ta hanyar amfani da farfaganda da kuma tada hankali wajen tilastawa gwamnatoci karba ko mika wuya ga bukatun siyasa ba sabon abu bane a duniya.”

Martanin Bello Yabo

A nasa martanin ga kalaman Garba Shehu, malamin ya caccaki mai magana da yawun shugaban kasar saboda bayyana bidiyon a matsayin shiri ko kuma farfaganda..

Ya zargi Garba Shehu da cewa bai damu da halin da masu garkuwa da mutane suka sanya mutane ciki ba, ya kuma yi addu’a ga Shehu ya fada hannun masu garkuwa da mutanen, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Wakilin Leigit.ng Hausa ya bibiyi wani bidiyo da ya yadu a kafar sada zumunta, inda Bello Yabo ke cewa:

“Muna yi musu addu’a masu kamen nan, ya Allah ya baku sa’a ya ku masu kamen nan, ku matsa za mu taimaka muku da addu’a Allah ya baku sa’a ku kamo shi. Wadannan da kuka ce za ku kama ALlah ya baku sa’a ku kamo su. Amma ku sako wadancan da ke hannunku.

“Idan da irinsu kuke kamawa mu wallahi albarka ma za mu sa muku don sun zama mana bala’i. Meye amfaninsu?”

Hakazalika, malamin ya kuma caccaki yadda gwamnatin Buhari ke tafiyar da lamurran rashin tsaro, a cikin wani bidiyon na daban.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here