Aikin da Mukai Kan ‘Yan Bindiga a Cikin Makon Nan – Rundunar ‘Yan Sanda

Rundunar ‘yan sanda ta bayyana aikin da ta yi kan ‘yan bindiga a cikin makon nan, inda ta ragargaji wasu a hanyar Birnin Gwani.

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, ‘yan bindigan sun dasa tarkon mugun nufi ga fasinjoji a kan hanyar.

Da nufin Allah, ‘yan sanda sun gano su, sun yi musayar wuta, inda da dama suka samu raunukan harbin bindiga.

Kaduna- Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna a ranar Litinin ta fatattaki wasu ‘yan bindiga da suka yi wa masu ababen hawa kwanton bauna a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Haka kuma sun kwato bindiga kirar AK47 guda daya da kuma babura guda hudu wadanda ba a yiwa rajista ba daga hannun ‘yan bindigar a yayin musayar wuta, Daily Trust ta rawaito.

Wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) a Kaduna, ASP Jalige Mohammed, ta ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 11:30 na safe.

A cewar sanarwar: “Jami’an rundunar ‘yan sandan Kaduna da ke aiki da shiyya ta Buruku a lokacin da suke sintiri a Udawa kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari sun yi taho-mu-gama da wasu ‘yan bindiga a kokarinsu na aikata mugun nufi a kan fasinjojin da ba su ji ba gani.

“Jami’an ‘yan sanda tare da ’yan banga sun nuna jarumtaka wajen mayar da wuta cikin tsanaki, inda suka yi nasarar dakile harin yayin da suka tilasta wa ‘yan bindigar tserewa da raunuka daban-daban zuwa dajin inda suka bar bindiga AK47 guda daya da kuma babura guda hudu marasa rajista.

“An kwato kayayyakin ne an kai su ofishin ‘yan sanda na Buruku yayin da ake kokarin gano inda ‘yan bindigan da suka jikkata suke domin fuskantar fushin doka.”

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Yekini A. Ayoku, ya yi kira ga al’ummomin da ke kewayen yankin da su sanya ido ga duk wanda aka gani da raunin harsashi, sannan su kai rahoto ga jami’an tsaro mafi kusa da su domin daukar mataki cikin gaggawa, inji Tori.ng.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here