Mifepristone: Kotu a Amurka ta Amince a Ci gaba da Amfani da Maganin Zubar da Ciki

Wata kotun ɗaukaka ƙara a Amurka ta dakatar da hukuncin da kotun Texas ta yi na ɗan lokaci, na dakatar da amfani da maganin zubar da ciki.

Mifepristone – na ɗaya daga cikin magunguna biyu da ake amfani da su wajen zuban da ciki waɗanda hukumar abinci da magunguna ta Amurka ta amince a riƙa amfani da su sama da shekara 20.

Yanzu dai amfi amfani da kwayoyi a matsayin magnin da ake amfani da su wajen zubar da ciki, kuma rabin cikkunan da ake zubarwa a Amurka ana amfani da su.

Wannan dai na nufin za a ci gaba da amfani da maganin amma akwai wasu ‘yan dokoki da za a riƙa bi.

Akwai buƙatar likita ya bayar da kwayoyin a kuma rage amfani da su a makonni bakwan farko na ciki zuwa 10 wanda aka amince da shi a yanzu.

Masu sukar alƙalin da ya yanke hukuncin Texas sun ce wannan zai bayar da damar ƙalubalantar sauran kwayoyin da aka amince da su a Amurka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here