Shugaban APC na Kasa ya Dakatar da Dukkannin Daraktocin Sakateriyar Jam’iyyar

 

Sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya dakatar da dukkannin daraktocin sakateriyar jam’iyyar.

Tun ranar da ya karba ragamar mulki, ya sanar da cewa ba zai yi amfani da tsoffin tsarika ba kuma ba zai lamunci gazawar aiki ba.

Daga cikin daraktocin da aka dakatar, akwai daraktocin gudanarwa, tsari, jindadi da walwala, shari’a da yada labarai.

FCT, Abuja – Wata sabuwa ta sake kacamewa a gidan Buhari inda hankula suka tashi a sakateriyar jam’iyyar APC ta kasa a ranar Juma’a sakamakon hukuncin shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu inda ya bukaci dukkan daraktocin jam’iyyar da su dakata da aiki har sai baba ta gani.

Bayan Adamu ya hau karagar shugabancin jam’iyyar a ranar 1 ga watan fairilu, ya bayyana cewa akwai yuwuwar ya sake gyara tsarin ssakateriyar jam’iyyar ta kasa.

A halin yanzu ya bazama gyara tsarin sakateriyar jam’iyyar inda ya mayar da ofishinsa kasa a maimakon hawa na uku da yake a baya.

A ranar 1 ga watan Afirilu, Adamu ya bayyana cewa akwai yuwuwar bincikar dukkan ma’aikatan sakateriyar ballantana daraktoci.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa jam’iyyar ba za ta cigaba da amfani da tsoffin tsarika na baya ba wurin gudanar da ayyuka, inda ya kara da cewa mulkinsa ba zai lamunci gazawa ba ko kadan.

A ranar Juma’a, Vanguard ta tattaro cewa, sakamakon shawarar kwamitin, Adamu ya yanke shawarar dakatar da dukkanin daraktocin sakateriyar, kusan su takwas.

Wasu daga cikin daraktocin sun hada da na gudanarwa, tsari, jindadi da walwala, shari’a da yada labarai.

Wannan hukunci na Adamu za a iya cewa shi ne farko da aka taba yi a sakateriya jam’iyyar APC.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here