Gwamna Ben Ayade ya Raba Kafa Gabanin Zaben Fidda Gwani da Babban Zaben 2023

 

Gwamna Ben Ayade na Kuros Riba ya yanke shawarar raba kafa gabanin fidda gwani da babban zaben 2023.

Matashi kuma hazikin gwamnan wanda dan takarar shugaban kasa ne a jam’iyyar APC, ya fara hango kujerar Sanata a jiharsa.

Hasali ma, Ayade ya ci gaba ta hanyar saya wa kansa fom tsayawa takarar sanata ta mazabarsa a jihar ta Kuros Riba.

Kuros Riba – Gwamnan jihar Kuros Riba, Ben Ayade, ya karbi fom din takarar Sanata mai lamba 9498 a karkashin jam’iyyar APC mai mulki, kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.

Gwamnan wanda ya karbi fom din sa a ranar 10 ga Mayu, 2022, zai tsaya takarar dan majalisar dattawa ta mazabar Arewa a jiharsa inda zai fafata tare Orim Martin Ojie wanda ya karbi fom a ranar 6 ga Mayu, 2022.

Jaridar ta ruwaito cewa wasu gungun mutane da aka fi sani da ‘ya’ya maza da mata na Kuros Riba, sun saya masa fom din tsayawa takara a jam’iyyar APC domin ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.

Gwamnan wanda ya bayar da tabbacin cewa zai magance matsalar rashin wutar lantarki gadan-gadan, ya ce a shirye yake ya samar da hanyar da za ta iya magance matsalar gaba daya kowa ya huta.

Dan takarar shugaban kasa a PDP, Bala ya lallaba ya sayi fom din gwamna

Ba Ayade kadai ba, yayin da Bala Mohammed ke cikin jerin ‘yan takarar shugaban kasa na PDP, a boye ya lallaba ya sayi fom din takarar komawa kujerar gwamnan jihar Bauchi a wa’adi na biyu, kamar yadda Premium Times ta ce ta samo.

Gwamna Mohammed dai zai cika wa’adinsa na farko a matsayin gwamnan jihar Bauchi ne a 2023, kuma zai iya sake neman takarar gwamnan a karo na biyu.

An sha hasashe kan wanda zai gaje shi a 2023 bayan da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a kwana nan.

Daya daga cikin irin wadannan hasashe ya nuna cewa sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Kashim ya shiga wata yarjejeniya da gwamnan domin ya zama mai rike masa da mukaminsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here