Masu Kaiwa ‘Yan Bindiga Bayanai Kan Sarkin Bungudu ke Hana Yunkurin Ceto Shi
Masu kaiwa yan bindiga bayanai ke hana ruwa gudu wajen yunkurin ceto mai martaba Sarkin Bungudu, Hassan Attahiru, duk da an biya kudin fansar milyan ashirin.
Yan bindiga sun yi awon gaba da Sarkin ne a titin Kaduna-Abuja ranar Talata, 14 ga Satumba, 2021.
Jaridar Punch ta rawaito hirar da tayi da wani na kusa da iyalan Sarkin wanda ya bayyana cewa akwai wani mai kaiwa yan bindigan bayanai.
Wannan mai kai bayanan ya fadawa yan bindigan cewa su kara neman kudi wajen iyalan Sarkin kuma yana bayyana duk wani tattaunawa da iyalan Sarkin keyi.
Yace:
“Da an saki Sarkin tuni amma akwai mai kai wa yan bindiga bayanai.”
“Wannan shine dalilin da yasa yan bindigan ke kara kudin saboda sun san abubuwan da muke tattaunawa.”
“Da farko sun bukaci N100m, amma bayan tattaunawa, sun sauko N20m kuma aka biyasu ba tare da bata lokaci ba.”
“Abinda ya bamu mamaki shine, yan bindigan sun ce sun samu labarin iyalan Sarki za su iya bayar da ko nawa ne don ceto Sarkin.”
Majiyan ya cigaba da cewa yanzu yan bindigan sun ce cinikin ya dawo sabo, N100m za’a biya kudin fansa idan har suna son a saki Sarki.
Yace:
“Kai har fada mana sukayi sun san yadda muka tara N20m din farko. Saboda haka muna cikin wani mugun hali.”