Allah ya Yiwa Tsohon ‘Dan Kwallon Super Eagles, Bello Musa Kofarmata Rasuwa

 

Allah ya yiwa Tsohon dan kwallon Super Eagles kuma Kano Pillars, Bello Musa Kofarmata, cikawa daren Talata, 2 ga watan Nuwamba, 2022.

Bello ya mutu ne yana dan shekaru 34 bayan jinyar da yayi a gidansa dake unguwar Kofarmata, Kano, rahoton Leadership.

Tsohon mataimakin shugaban kungiyar marubuta labaran kwallo a Najeriya SWAN, Ado Salifu, ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.

Ya ce an yi jana’izarsa da safiyar Laraba a unguwar Kofarmata bisa koyarwan addinin Musulunci.

Kofarmata ya na cikin gwanayen yan kwallon da suka taya Kano Pillars lashe gasar Firimiyar Najeriya a 2007/2008 inda yaci kwallaye 11 a kakar.

Shine mutum mafi yawan kwallaye a shekarar. Bayan barin Kano Pillars a 2010, marigayin ya koma kungiyar kwallon Heartland a Owerri kafin komawa Elkanemi a 2012.

Bayan kankanin lokaci ya koma Kano Pillarsa sannan ya samu shiga kungiyar kwallon IK Start dake Norway.

Marigayin na cikin yan kwallon Najeriya U20 da suka taka leda a gasar kofin kwallon duniya da aka buga a Kanada 2007.

A 2010, ya bugawa Super Eagles wasar zumunta da Kongo guda a Abuja inda Najeriya ta lallasa DRC 5-2.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here