Brighton na Shirin kammala Yarjejeniyar ɗauko Ansu Fati Daga Barcelona

 

Dan wasan gaba na kasar Sifaniya Ansu Fati na shirin kammala yarjejeniyar aro na tsawon kakar wasa daya zuwa Brighton daga Barcelona.

Fati ya rasa gurbinsa a Barcelona, ​​wadda ke bukatar samar da wuri a tawagar ‘yan wasanta don samun damar dauko aron dan wasan baya na Manchester City Joao Cancelo.

Yarjejeniyar Brighton na dan wasan mai shekaru 20 bai hada da wajibcin siya ba.

Tottenham na cikin jerin masu son daukan Fati amma an fahimci cewa dan wasan ya fi sha’awar salon wasan Brighton a karkashin koci Roberto de Zerbi.

Idan yarjejeniyar ta gudana kamar yadda aka tsara, zai zama babban yunkuri a bangaren Brighton, wadda za ta buga gasar nahiyar Turai a kakar wasan bana bayan ta samu gurbin shiga gasar cin kofin Europa.

Fati, wanda aka haifa a Guinea-Bissau amma ya zabi ya wakilci kasar Sifaniya kuma yana cikin tawagar da ta wakilci kasar a gasar cin kofin duniya a bara, ana kallon sa a matsayin daya daga cikin matasan ‘yan wasa da za su taka rawar gani a fagen wasan kwallon kafa.

A 2021, ya sanya hannu kan sabuwar kwantiragi da Barcelona don ci gaba har zuwa 2027.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com