Ni Kadai ne Zan Iya Cin Galaba Akan APC – Gwamna Wike

Gwamnan Jihar Ribas kuma dan takarar shugaban kasa karkashin PDP, Nyesom Wike ya ce shi kadai ne zai iya cin galaba akan APC.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Lokoja yayin jawabi ga wakilan PDP inda ya ce APC ta yi huji mai zurfi a kasar nan wanda sai dan siyasa mai karfi ne zai iya cikasa gurbin.

Kamar yadda ya ce, kasar nan ta fuskanci rabe-rabe sakamakon rashin tsaro har a jihar shugaban kasa, don haka shi kadai ne ya ke da damar da zai iya ceto Najeriya.

Jihar Kogi – Nyesom Wike, gwamnan Jihar Ribas sannan dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar PDP ya ce shi ne kadai ne zai iya kai APC kasa, The Punch ta ruwaito.

Ya bayyana haka ne a Lokoja yayin jawabi ga wakilan jam’iyyar inda Wike ya ce APC ta haka rami mai zurfi a kasar nan don haka samun shugaban kasa mai halaye masu kyau da kuma karfi a siyasa ne kadai zai fitar da kasar daga cikin ramin.

Ya ce kowa ya mayar da hankali akan wannan zaben mai zuwa

Kamar yadda The Punch ta nuna, Wike ya ce:

“Wannan kasar ba ta taba fuskantar matsalolin tsaro masu yawa ba kamar yanzu, har ta kai ga garin su shugaban kasa ma ba a bar shi a baya ba. Don haka Najeriya tana neman wanda zai ceto ta.

“Wannan zaben shi ne ko wanne dan Najeriya ya dace ya mayar da hankali akan shi. Wajibi ne mu hada kai don babu wanda zai iya yi shi daya; shugaban kasar da zai amshi mulki ne zai dage wurin amfani da abubuwan da ke hannu don kawo gyara a kasa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here