Dakyar na Sha Yayin da Ake Zaben Fidda Gwanin Gwamnoni – Sha’aban Sharada

Sha’aban Sharada, dan takarar gwamnan Jihar Kano, karkashin jam’iyyar APC ya bayyana dalilinsa na barin wurin zaben fidda gwani, kuma ya ki amincewa da sakamakon.

Sharada ne kadai dan takarar da ya kalubalanci gabatar da mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Gawuna a matsayin dan takarar da gwamna ya marawa baya a farkon watan Mayu.

Sharada ya saki wata takarda a ranar Juma’a wacce ya ce dakyar shi da wasu masu mara masa baya su ka tsira saboda an kusa kai musu farmaki a kuma halaka su.

Kano- Dan takarar gwamna karkashin inuwar jam’iyyar APC, Sha’aban Sharada, ya bayyana dalilinsa na barin inda ake zaben fidda gwanin jam’iyyar APC, kuma ya kalubalanci sakamakon zaben.

Sharada ne dan takara daya da ya nuna rashin amincewarsa akan gabatar da mataimakin gwamnan jihar, Nasir Gawuna, a matsayin dan takarar gwamna a farkon watan Mayu, rahoton The Cable.

A wata takarda wacce Daily Nigerian ta saki ranar Juma’a, Sharada ya ce dakyar shi da wasu mabiyansa su ka sha daga harin da aka kai musu.

Sharada ya ce an ja kunnensa akan zuwa wurin zaben

Kamar yadda ya ce:

“Dakyar na sha yayin da ake zaben fidda gwanin gwamnonin da aka yi yau a Kano. Ana saura mintoci kadan a fara zaben, wani jami’in tsaro ya ja kunne na akan zuwa wurin da ake zaben. Daga nan shugaban kwamitin zaben fidda gwanin jam’iyyar, Sanata Tijjani Kaura ya tura min sako inda ya bukaci in je wurin.

“Abinda ya ba ni mamaki shi ne yadda aka dakatar da jami’an tsaron da aka turo tun daga Abuja raka ni wurin da za a yi zaben. Daga nan wani ya sanar da ni cewa ana ta yada batun yunkurin halaka ni saboda kada in lashe zaben. Hakan ya sa na dauki matakan tsaro na shiga wurin zaben, ina godiya ga Allah (SWT).

“A jawabin da na yi, na ja hankalin duk masu ruwa da tsaki akan shirin gwamnatin Jihar Kano na tilasta dan takara ga jam’iyyarmu, inda na shawarci wakilai da su yi amfani da ‘yancinsu da kundin tsarin mulki ya ba su na zaben wanda su ke so. Ba a yi zabe ba.”

A cewarsa, yayin da ake tsaka da zaben, an ci gaba da shirye-shiryen kai masa farmaki, ana so a halaka shi da zarar ya bar wurin.

Daga baya ya kara samun bayani akan yadda aka halaka wasu masu mara masa baya tare da ji wa wasu raunuka wanda hakan ya sa ya yi gaggawar barin wurin su ka zarce asibiti don a duba lafiyarsu.

Ya nemi jami’an tsaro su yi bincike akan kashe-kashen

Ya ce a wurinsa rayuwar mutum daya ta fi masa muhimmanci akan zama gwamna. Hakan ya sa ya yi kira ga jami’an tsaro akan yin bincike mai zurfi tare da hukunta wadanda su ka yi wannan aika-aikar.

Ya kuma yi kira akan a rushe zaben fidda gwanin da aka ce an yi, don bai nuna nagartar babbar jam’iyya irin APC ba kuma ba haka demokradiyya ta ke ba.

Ya yi wa wadanda su ka rasa rayukansu fatan samun rahamar Ubangiji tare da yi wa marasa lafiyar da su ka samu raunuka fatan samun lafiya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here