Dalilin da Yasa na Waskawa Matar Gwamna Obiano Mari – Matar Ojukwu

Ambasada Bianca Ojukwu, matar marigayi Chukwuemeka Ojukwu ta bayyana abinda ya faru tsakaninta da matar tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano.

Yayinda bikin rantsar da sabon gwamnan jihar Anambra Ebelechukwu Obiano da Bianca sun baiwa hammata iska.

A jawabin da ta saki ranar Juma’a, ta bada labarin abinda ya faru.

Tace:

“Abin mamaki, ta durfafo ni. Na yi tunanin gaishe dani tazo yi. amma kawai sai ta fara zagi na tana daga murya, tana tsokanata tana tambayata me ya kawo ni.”

“Amma na share ta. Sai ta fara daura hannu kan kafada ta tana daga murya. Sai nace ta daina taba ni amma taki dainawa, ta fara kokarin cire min dan kwali. Wannan rainin hankali ne ga babbar mace iri na a al’adar Igbo.”

“A lokacin na mike don kare kaina kuma na waska mata mari don ta daina taba ni.”

Abinda ya bani mamaki shine a buge take da giya. Na yi mamakin jin warin giya bakinta. Ta yaya uwargidar gwamna zata shigo taron rantsarwa a buge misalin karfe 9 na safe.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here