An Naɗa ɗan Najeriya a Matsayin Kocin Tawagar ‘Yan Wasan Amurka

 

An naɗa tsohon mai bugawa Najeriya, Michael Nsien, a matsayin kocin tawagar ‘yan wasan Amurka ajin matasa ‘yan kasa da shekara 16.

An sanar da naɗin Nsien a shafukan wasanni na Amurka.

Nsien mai shekara 41 haifafen yankin Tulsa ne da ke jihar Oklahoma ta Amurka, kuma yana cikin tawagar ‘yan Super Eagles ajin kasa da shekara 23 da suka gaza zuwa gasar Olympic ta 2004 a Athens.

Dan kwallon na da kwarewa sosai na tsawon shekara 12 da ya shafe yana horar da ‘yan wasa a jiharsa kafin ya samu lasisin UEFA.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here