Daukar Tubabbun Boko Haram: Rundunar Sojojin Najeriya ta Karyata Jita-Jitar

 

Rundunar sojojin Najeriya ta karyata jita-jitar cewa rundunar za ta dauki tubabbun ‘yan ta’addan Boko Harm.

Wannan na zuwa ne bayan da rundunar ta ce ta gano wani bidiyo dake nuna yunkurin hakan a kafafen sada zumunta.

Rundunar ta ce ba ta da niyyar daukar wasu tubabbun ‘yan Boko Haram ta kowa ce fuska a kasar.

Abuja – Rundunar Sojin Najeriya ta ce ba za ta dauki tsoffin ‘yan ta’adda masu tayar da kayar baya a cikin rundunar sojojin Najeriya ba, The Cable ta rawaito.

Kakakin rundunar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata 24 ga watan Agusta a babban birnin tarayya Abuja.

Nwachukwu ya ce hankalin sojoji ya je ga wani bidiyo da wani matashi ya watsa a kafafen sada zumunta kuma Anthony Jay ya shirya wanda ya danganta rugujewar sojojin Afghanistan da mika wuya ga mayakan Boko Haram a Najeriya.

Ya ce Young Elder, cikin raha, ya nuna damuwar sa game da maharan da suka mika wuya.

A cewar Onyema:

“Duk da yake an fahimci cewa halin da ake ciki a Afghanistan abin damuwa ne ga duk wani mai tunani ko kungiya mai tunani, yadda Young Elder ya gabatar da hakan yana nuna karancin iliminsa kan batun da ya yi wa hawan kawara.”

“Karancin ilimin da ke ciki ya haifar da wasu maganganu marasa tushe kuma marasa asali wadanda kawai ke cikin tunaninsu, suna masu cewa ‘yan ta’adda da suka mika wuya za su shiga cikin Sojojin Najeriya.

“Don nisantar shakku, NA ba ta da wani dan ta’adda da ya tuba da zai shiga sahu kuma ba ta da wani shiri na yin hakan.

“Akwai ‘yan Najeriya masu karfin gwiwa wadanda ke son shiga cikin NA don taimakawa da gaske wajen yakar ta’addanci da sauran manyan laifuka.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here