A Janye Karin Kudin Fetur: DSS ta Mamaye Ofishin SERAP

 

Abuja – Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun karbe ikon ofishin kungiyar kare hakkin al’umma da tattalin arzikin kasa (SERAP) da ke babban birnin tarayya Abuja.

Mamaye ofishin SERAP da jami’an DSS suka yi na zuwa ne awanni bayan da kungiyar ta nemi Shugaba Bola Tinubu ya janye karin kudin fetur da kuma bincikar NNPCL.

DSS sun mamaye ofishin SERAP

Kungiyar SERAP ce ta sanar da wannan samamen da jami’an DSS suka kai ofishinta a shafinta na X a ranar Litinin.

Kungiyar ta bayyana cewa kwace ikon ofishinta da DSS ta yi ya sabawa dokar kasa.

SERAP ta ce jami’an hukumar DSS bayan mamaye ofishinta, sun bukaci ganawa da daraktocin kungiyar.

Kungiyar ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya sa baki a wannan lamari.

SERAP ta nemi daukin Tinubu

Sanarwar da SERAP ta fitar ta ce:

“A halin yanzu jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) sun mamaye ofishin SERAP da ke Abuja ba bisa ka’ida ba, suna neman ganin daraktocin mu.

“Ya zama wajibi Shugaba Tinubu ya umarci hukumar SSS da ta gaggauta kawo karshen wannan cin zarafin, da kuma farmaki ga ‘yancin ‘yan Najeriya.”

“A janye karin kudin fetur” – SERAP

Tun da fari, mun ruwaito cewa kungiyar da ke kare hakkin al’umma da tattalin arzikin kasa (SERAP) ta ba Shugaba Bola Tinubu wa’adin awa 48 ya janye karin kudin fetur.

SERAP ta kuma bukaci shugaban kasar da ya kaddamar da binciken cin hanci da rashawa a kamfanin NNPCL wanda ta ce shi ne ke jawo cikas ga bangaren man kasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here