Bama Goyan Bayan Ballewa Daga Najeriya – Kungiyar BRAC

 

Kungiyar BRAC a kudu maso kudu ta bayyana cewa ba ta goyon bayan ballewa daga Najeriya.

Kungiyar ta bayyana bata tare da haramtacciyar kungiyar nan ta fafutukar kafa kasar Biafra.

Kodinetan kungiyar ta BRAC ce ta bayyana hakan a ranar Lahadi a wani taro a birnin Abuja Kungiyar ‘yan asalin yankunan gabar teku na Bayelsa, Ribas, Akwa Ibom da Kuros Riba (BRAC) sun ce ba sa goyon bayan yunkurin neman ballewa daga Najeriya.

Sun kuma ce ba sa cikin ayyukan haramtacciyar kungiyar nan ta fafutukar ‘yanta ‘yan asalin Biafra. Kodineta na BRAC, Doris McDaniels, ta bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja ranar Lahadi.

Doris, ta bayyana alakar yankunan da gabar tekun da ya hada kabilu marasa rinjaye na tsohuwar yankin gabashin Najeriya wanda ya raba yankunan BRAC da na Biafra.

Daily Trust ta ruwaito tana cewa, “Bari na fada karara cewa duk da cewa BRAC ba ta da niyyar ballewa daga yankin Kudu-maso-kudu, amma mambobin kungiyar ba su cimma wata nasara ba a karkashin inuwar yankin Neja Delta.

“Babu wani ajanda gama gari da za mu dogara da shi, don tsara ci gaban yanzu da kuma nan gaba ga mutanenmu da yankin gabar teku.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here