Gwamnatin Tarayya na Shirin Rattafa Hannu Kan Sabon Bashin $3.387bn Don yin Ayyuka 10 – Zainab Ahmed

Ministar kudi, kasafin kudi, da shirye-shiryen kasa, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin rattafa hannu kan sabon bashin $3.387 billion don yin wasu ayyuka 10 a fadin tarayya.

Ministar ta bayyana hakan a taron da ma’aikatar labarai da al’adu ta shirya kan nasarorin da Gwamnatin tarayya ta samu kan manyan ayyukan cigaba, rahoton Tribune.

Ga jerin ayyukan da tace za’ayi da kudin dan aka karbo bashin:

1. Layin dogon zamani na cikin birnin Kano (Aikin farko): US$673.2 million,

2. Ginin titin Lafia By-Pass da fadada 9th Mile (Enugu)-Otukpo-Makurdi :

3. Samar da hanyar tsaron boda na zamani: US$175.5 million.

4. Aikin wutan lantarkin Najeriya (Off-Grid): US$350 million,

5.Aikin isar da lantarki (karkashin West African Power Pool): US$32.3 million,

6. Aikin wutan lantarki : US$486 million.

7. Aikin lantarkin dinke Najeriya: US$200 million,

8. Fadada hanyoyin raba wutan lantarki (karkashin Bankin cigaban Afrika AfDB): US$210 million

9. Shirin rabon wutan lantarkin birnin tarayya Abuja: US$170 million,

10. Aikin layin wutan lantarkin Arewa (Bankin cigaban Faransa): $245 million

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here