Gwamnonin Jam’iyyar APC Sun Yabi Jagorancin Mai Mala Buni

 

Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki sun kaɗa kuri’ar amincewa da jagorancin kwamitin riko na Buni.

Gwamnonin sun ce hukuncin kotun koli na zaɓen gwamnan Ondo ya kara tabbatar da cewa kwamitin na kan tsarin doka.

Hakanan sun ce kwamitin da takwaransu Mai Mala Buni yake jagoranta yana aiki mai kyau wajen shirya APC gabanin zaɓen 2023.

FCT Abuja – Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki sun kaɗa kuri’ar amincewa da kwamitin rikon kwarya wanda takwaransu gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, yake jagoranta, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamnonin sun bayyana cewa hukuncin da kotun koli ta yanke a kan zaɓen gwamnan jahar Ondo ya nuna cewa kwamitin na kan doka.

Gwamnonin sun yi wanna jawabin ne a taron da suka gudanar ranar Litinin domin tattauna matsalolin da suka taso a jam’iyyar.

Taron wanda ya gudana a gidan gwamnan Kebbi dake Asokoro, ya samu jagorancin shugaban ƙungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu, kamar yadda leadership ta ruwaito.

Kwamitin rikon kwarya ya sha yabo

Gwamna Atiku Bagudu yace kwamitin rikon kwarya bisa jagorancin Mai Mala Buni ya yi namijin kokari wajen saita jam’iyyar ta APC.

A jawabinsa yace:

“Kwamitin rikon kwarya bisa jagorancin Buni ya yi aiki mai kyau wajen saita APC da kuma kara wa jam’iyyar karfi da shiri yayin da zaɓen 2023 ke kara gabatowa.”

Taron ya kara jaddada cewa amincewar gwamnonin APC zai kara wa jam’iyyar karfin guiwa wajen cigaba da garambawul ɗin da take yi.

Hakanan zai taimaka wajen saita jam’iyyar ta hanyar ƙara mata karfi yayin da ake cigaba da tarukan APC a faɗin kasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here