Manyan ‘Yan Najeriya Masu Fada a Aji 20 da Suka Halarci Daurin Auran ‘Dan Shugaba Buhari
Manyan jiga-jigan siyasan Najeriya sun dira kasar Bichi, a jahar Kano domin halartan daurin auren ‘dan Buhari daya tilo, Yusuf, da diyar sarkin Bichi, Zahra Bayero.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ibrahim Pantami, ne ya daura aure a Masallacin kasar Bichi.
Yayinda babban attajiri, Alhaji Aminu Dantata, ya bada auren a madadin iyalan Sarkin Bichi; dan uwa kuma babban aminin Buhari, Malam Mamman Daura, ya karba aure matsayin wakilin ango kuma madadin shugaba Buhari.
An dade ba’a daurin auren da ya tattara manyan masu fada a aji irin wannan ba.
Ga jerin wasu sannannu da suka halarci daurin aure:
1. Shugaba Muhammadu Buhari
Read Also:
2. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo
3. Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
4. Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar
5. Tsohon shugaban kasan jamhurriyar Nijar, Mohammadou Issoufou
6. Alhaji Aminu Dantata
7. Malam Mamman Daura
8. Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Ganduje
9. Shugaban kungiyar gwamnoni kuma gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi
10. Gwamnan jahar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.
11. Gwamnan jahar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal
12. Gwamnan jahar Jigawa, Muhammad Badaru Talamiz
13. Gwamnan jahar Yobe, Mai Mala Buni
14. Mataimakin gwamnan Kano, Yusuf Gawuna
15. Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle
16. Gwamnan Borno, BabaganMai a Umara Zulum
17. Sanata Ahmad Sani Yarima
18. Sanata Ali Ndume
19. Malam Nuhu Ribadu
20. Shugaban masu rinjaye a majalisa, Ado Doguwa