An kai Harin Bom a Masallacin Babban Birnin Afghanistan

Mutane da dama sun mutu a wani harin bom da aka kai a masallaci a Kabul babban birnin Afghanistan.

Kakakin gwamnatin Taliban Zabihullah Mujahid ya tabbatar da harin a Twitter inda ya ce bom ɗin ya tashi a ƙofar shiga Masallacin Idqa.

Rahotanni sun ce an kai harin ne lokacin da ake gudanar da addu’o’i a masallacin ga mahaifiyar Zabihullah Mujahid wacce ta rasu a makon da ya gabata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here