Sai Bayan Gwamnatin Buhari Igboho Zai Dawo Najeriya – Lauya

 

Gwamnatin Najeriya na cigaba da kokarin dawo da Sunday Igboho Najeriya.

Jami’an tsaro a Kotono sun damkeshi yayinda yake kokarin guduwa Jamus.

Hukumar DSS ta alanta neman Igboho ruwa jallo bayan da ta kai hari gidansa.

Daya daga cikin lauyoyin Sunday Igboho, mai rajin kafa kasar Oduduwa, Olusegun Falola, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya zama shugaban kama karya.

Ya kara da cewa zaman da Igboho ke yi a jamhuriyyar Benin alheri ne gare sa.

Lauyan yace Sunday Igboho bai zai dawo Najeriya ba har zai bayan karewar wa’adin mulkin shugaba Buhari.

Falola ya bayyana hakan a wata hira da gidan rediyo kuma The Nation ta rawaito.

Igboho ya kwashe wata guda a kurkuku kasar Benin tun lokacin da aka damkeshi ranar 19 ga Yuli, 2021 a Kotonou.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here