Mayakan ISWAP Sun Kashe Jami’an Tsaro da Farar-hula a Borno
Mayakan jihadi sun kai hari sansanin soji da wani yankin Borno tare da kashe sojoji 9, da ‘yan sanda biyu da kuma farar-hula, kamar yada majiyoyin tsaro da mazauna yanki suka tabbatar.
Mayakan IS sun farwa garin Malam Fatori, a ranakun daren Juma’a da kuma safiyar Asabar, a cewar majiyoyin.
Read Also:
A cewar bayanan da aka fitar, an tafka asara sosai a harin.
Harin na farko, a kusa da iyakar Najeriya da Nijar anyi ɓarin wuta sosai tsakanin sojoji da mayakan, a cewar Buji Garwa.
A watan Maris da ya gabata ne, dubban mutane da rikicin Boko Haram ya tilastawa tserewa zuwa Nijar, suka dawo yankunansu a Malam Fatori.
Wani babban jami’in Ukraine Kyrylo Tymoshenko, ya ce ma’aikata na can na duba wadanda harin da ya rutsa da su.