Jaafar Jaafar Ya Yaba Aikin Da Jaridar Arewa Agenda Keyi
Shahararre kuma kwararren Dan jaridar nan Ja’afar Ja’afar ya yaba aikin da Jaridar Arewa Agenda take yi wajen kawo cigaba a cikin Al’umma.
Jaafar Jaafar ya bayyana hakan ne a wata ziyara da tawagar ma’aikatan Jaridar suka kai masa a ofishin sa dake Jihar Abujar Najeriya, a inda ya kara Jaddada aikin jarida a matsayin wata hanya ta bayyanawa Al’umma gaskiya, tare da shawaratar a cigaba da amfani da wanna kafa ta sadarwar zamani domin kawo cigaba mai dorewa ga Al’umma a harkokin su na yau da kullum.
Read Also:
Hakazalika,ya kara da cewa ,Gaskiya ita ce kan gaba wajen gudanar da aikin na Jarida, jajircewa da aiki tukuru wajibi ne domin cimma kyakkywar manufa. Fadar gaskiya komai dacinta shine ribar aikin Jarida mafi kyawu,tare da cewar hakan na da mutukar hadari a cikin aikin na jarida duba da irin barazanar da ake samu, amma tsaya tsam akan turbar gaskiyar itace mudubin dukkan cigaba mafi alfanu.
Shima anasa bangaren,Dan jarida Kuma masani a fannin shawo kan rikici da tarzoma a kasar nan, Mr. Chidi Jude Omeje yayi kira ga Jaridar ta Arewa Agenda data zama cibiya wajen duba al’amuran dake damun Arewacin kasar Nan dama sauran sassan kasar baki daya. Mr. Chidi ya kara da cewar Jaridar ta Arewa Agenda data cigaba da hada gwiwa da sauran yankun kasar domin kawo cigaba mai karfi a yanki na Arewacin Najeriya da kasa Baki daya.
A karshe, kwararren dan jarida Ja’afar Ja’afar ya shawarci jaridar ta Arewa Agenda dasu bi duk wata hanya wajen bayyana sako mai inganci,tare bin dokar aikin jarida bisa ka’da, gami da cire tsoro,kana da Kuma fadin gaskiya a kowane hali, ya rufe da yimusu fatan samun nasara a dukkan al’amarun da suka saka a gaba.
Arewa Agenda Jarida ce ta matasan marubuta daga Arewacin Najeriya domin inganta zaman Lafiya da cigaban kasa ta hanyar hanyar kawo managartan labarai.