Jami’an Tsaron Najeriya Sun Nuna Jajircewa, Sun Cancanci Yabo – Lai Mohammed

Gwamnatin tarayya tace kowace rana Najeriya na ƙara samun aminci da zaman lafiya ta kowane ɓangare.

Ministan yaɗa labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce jami’an tsaron Najeriya sun nuna jajircewa, sun cancanci yabo .

Ministan ya yi bayanin yadda gwamnatin tarayya ta taimaka wa jami’an tsaro da kayan aiki har ake samun nasara.

Abuja- Gwamnatin tarayya tace Najeriya na samun zaman lafiya da aminci kowace rana tare da nasarori a yaƙin da take da Boko Haram/ISWAP, yan bindiga da sauran ayyukan ta’addanci.

Ministan yaɗa labarai da Al’adu, Alhaji Lai Muhammed, ne ya faɗi haka a wurin taron manema labarai a Abuja ranar Litinin, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Yace dakarun tsaro a Najeriya sun zafafa yaƙi da yan bindiga kuma suka jefa su cikin halin gudun ɓuya yayin da kullum ake ƙara tarwatsa sansanonin su.

A jawabinsa ya ce:

“Ina alfahari da jami’an tsaron mu maza da mata dake cin ɗamara, duk da taɓarɓarewar ƙalubalen tsaro, ba su karaya ba kuma sun jajirce.”

“A dai-dai lokacin da suka tarwatsa yan ta’addaa sansanonin su, wasu dubbanni tare da iyalansu na miƙa wuya tare da aje makamai.”

“Hukumomin tsaro sun tsaya da digadigan su ne bisa jagorancin da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ke samar musu da kuma sadaukarwan jami’an tsaro da shugabannin su.”

Yadda FG ta samar da kayan aiki

Muhammed ya bayyana cewa sama da sojoji 1,500 aka ɗauka aiki a rundunar sojin ruwa cikin shekarar nan yayin da sojojin sama (NAF) suka karɓi sabbin jiragen yaƙin Super Tucano 12 da JF-17 Thunder Fighter guda uku.

Ya ce dakarun sojin sun yi amfani da jiragen wajen luguden wuta ta sama, taimakawa sojin ƙasa, da kuma lalata sansanonin yan bindiga da makamansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here