Babban Alkalin FCT, Justice Salisu Garba Ya yi Murabus Bayan an Nadashi a Matsayin Mai Gudanarwa na NJI
Babban alkalin FCT, Justice Salisu Garba, ya yi murabus da kanshi tun bayan nadin da aka mishi a matsayin mai gudanarwa na NJI.
An samu wannan labarin ne a wata takarda wacce hadimin CJN din, Ahuraka Isah ya gabatar a ranar Litinin.
Kamar yadda takardar ta tabbatar, Justice Garba ya yi murabus ne da kansa tun bayan samun wannan mukami.
Sabon babban alkalin FCT, Justice Salisu Garba ya yi murabus da kanshi bayan an nadashi a matsayin mai gudanarwa na NJI.
An samu wannan sanarwarne a wata takarda wacce hadimin CJN na fannin yada labarai, Ahuraka Isah ya gabtar a ranar Litinin, Daily Nigerian ta ruwaito.
Read Also:
A cewarsa, NJIBG, Karkashin shugabancin babban alkalin Najeriya, CJN, Justice Tanko Muhammad, ta amince da nadin Garba.
Justice Garba, wanda shine babban alkalin FCT har zuwa lokacin da yayi murabus zai cigaba da aiki a NJI.
An rantsar dashi a matsayinsa na babban alkalin FCT a ranar 7 ga watan Yuni kuma ya kamata yayi murabus ne a ranar 10 ga watan Oktoba lokacin da zai cika shekaru 65.
An haifi Garba ne a ranar 10 ga watan Oktoban 1956 a karamar hukumar Malumfashi dake jahar Katsina, Daily Nigerian ta ruwaito.
An rantsar dashi a matsayin lauya a 1984 kuma ya kammala bautar kasarsa a 1985. Ya cigaba da aikinsa a matsayin lauya na tsawon shekaru 3 bayan bautar kasarsa.
An nada shi a matsayin alkalin kotun majistare dake Abuja a 1989 sannan ya yi aiki a matsayin rijistira a babbar kotu dake Abuja a 1998.