Kalaman Yaudara da Rashin Hankali Daga Bakin Mayaudari Kuma Sha-Sha-Sha – Fani-Kayode ga Shekarau

 

Diraktan kafafen ra’ayi da sada zumunta na kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar All Progressives Congress APC, Femi Fani-Kayode ya yi dirar Mikiya kan tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau.

Wannan ya biyo bayan jawabin da Malam Ibrahim Shekarau yayi kan lafiyar dan takarar shugaban kasan jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.

Shekarau ya bayyana cewa Tinubu fa ba isasshen lafiya garesa ba kuma kada a zabesa matsayin shugaban kasa.

Yace:

“Shin karya muka yi da muka ce yana fama da matsanancin rashin lafiya? Ta wani dalili zaku zabeshi matsayin shugaban kasa.”

Fani Kayode yayi martani

Femi Fani-Kayode ya yi martani mai zafi kan Shekarau inda ya kira shi da sha-sha-sha kuma ya tsine masa albarka.

A cewar Fani-Kayode, Atiku ne mara lafiya kuma ko zama a Najeriya ba ya yi, kasar Dubai yake zama.

Yace:

“Kalaman yaudara da rashin hankali daga bakin mayaudari kuma sha-sha-sha.”

“Allah sa Aradu ta ya kashe ka. Atiku ne mara lafiya ba Asiwaju ba. Bamu bukatan mata-maza wanda ke zama a Dubai. Mutumin kwarai irin Tinubu muke bukata.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here