Tsere wa Daga Zamfara Zuwa Neja: An kashe ‘Yan bindiga 32, ‘Yan sanda 5 Sun Rasu
Rundunar tsaron Najeriya ta ce an kashe ‘yan bindiga 32 a wasu hare-haren da ta kai kan maharan da ke tserewa Zamfara zuwa cikin jahar Neja.
Jaridar PRNigeria ta kuma rawaito cewa an kashe ‘yan bindigar ne bayan harin da suka kai a shingen binciken jami’an tsaro da sanadi rayukan ‘yan sanda 5.
Lamarin ya faru ne a yankin Bangu Gari da ke karamar hukumar Rafi ta Jahar.
Mijiyar tsaro ta tabbatarwa PRNigeria cewa maharan da ke tserewa Zamfara saboda tsananin hare-hare, na tada zaune tsaye a yankunan Neja.
Gungun maharan dauke da manyan makamai ciki harda roka na tserewa maboyarsu da ke Danjibga da Munhaye na karamar hukumar Tsafe da ke Zamfara.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here