Bayan Komawarsa APC: Lokaci ya yi da Zan Hada Kai da Shugaban Kasa Wurin Ciyar da Najariya Gaba – Fani Kayode

 

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya sha alwashin tarkata gwamnonin jahohin Oyo, Bauchi da na Enugu zuwa jam’iyya mai mulki bayan komawarsa a yau.

Gwamnan jahar Yobe, kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni ne ya gabatar da tsohon ministan ga shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Gwamna Bello Matawalle na jahar Zamfara.

Fani-Kayode wanda ya zanta da manema labarai, ya ce lokaci yayi da ya dace ya hada kai da shugaban kasa wurin ciyar da Najeriya gaba, Daily Nigerian ta rawaito.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here