Matar da ta yi Kokawa da Damisa Domin Ceto ‘Danta da Indiya

 

Indiya – Wata mahaifiya ta yi kokawa da damisa da hannunta domin ceto danta mai rarafe daga bakin damisa, kamar yadda jami’ai suka sanar ranar Laraba, rahoton Channels TV.

Archana Choudhary ta fita daga gidanta da ke Madhya Pradesh a daren ranar Lahadi saboda yaronta dan shekara daya da wata uku yana son yin fitsari.

Wani damisa da ake kyautata zaton ya tsere ne daga gandun daji na Bandhavgarh ya afka musu, jami’i Sanjeev Shrivastava ya shaidawa AFP.

Ta kai musu hari ya yi kokarin cizon kan yaron amma mahaifiyar ta tunkare shi don ceto danta, in ji shi.

Damisan ya cigaba da kokarin kwace yaron har sai da mazauna kauyen suka ji ihunta suka kawo mata dauki.

Daga nan ne damisan ya tsere ya shiga daji.

Shrivastava ya ce:

“An kwantar da ita a asibiti. Yanzu ta fara samun sauki. Jinjirin shima yanzu yana samun sauki.”

Mahaifiyar ta samu rauni a kirji da cikinta yayin da shi kuma danta akwai raunin cizo a kansa.

Jaridar Times of India ta ce an fara neman daminsan da nufin mayar da shi gandun dajin an kuma bukaci mazauna kauyen su dena fitowa waje cikin dare.

Dakaci karin bayani …

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here