NARD: Kungiyar Likitoci Za ta Shiga Yajin Aiki

 

Ƙungiyar Likitocin ƙasar nan NARD ta bayyana cewa zata tsunduma cikin yajin aiki matuƙar gwamnati bata biya su haƙƙokin su ba.

Ƙungiyar ta baiwa gwamnati wa’adi zuwa ƙarshen watan Maris ta yi abinda ya kamata ko su shiga yajin aiki.

Kuma sun buƙaci abiya su ragowar albashin su da aka riƙe musu da kuma kuɗaɗen inshora ga likitocin da suka rasa rayuwarsu a bakin aiki.

Ƙungiyar likitoci mazauna ƙasar nan sun yi barazanar zasu tsunduma yajin aiki matuƙar gwamnatin ƙasar nan bata biya musu buƙatunsu ba.

Ƙungiyar tace zata saurari gwamnati daga nan zuwa ɗaya ga watan Afrilu idan ba’a biya musu buƙatun su ba zasu shiga yajin aiki, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar bayan babban taron ta na ƙasa, ƙungiyar ta bayyana cewa buƙatun nata sun haɗa da biyan likitoci albashin su da aka riƙe.

Da kuma biyan albashin watan Maris da muke ciki kafin 31 ga watan Maris ɗin.

Sauran buƙatun sun haɗa da:

biyan mambobin ƙungiyar hakkoƙin su da suke bin bashi harda na watan Maris musamman na jihohi da kuma ma’aikatan lafiya na makarantun gaba da sakandire.

Da kuma biyansu kuɗaɗen su na aikin haɗari da suke yi, 50% na asalin albashin ma’aikatan lafiya da kuma kuɗaɗen su na COVID19 musamman a jahohin ƙasar nan.

Ƙungiyar likitocin na cikin gida NARD ta kuma yi kira da a canza shugaban likitoci na (MDCN) saboda gazawar sa wajen gudanar da aikinsa yadda ya kamata.

Hakan zai bada cikakkiyar damar aiwatar da gyaran tsarin likitocin cikin gida ba tare da wani tsaiko ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here