Karar Kwankwaso ga EFCC: Kakakin Darikar Kwankwasiyya ya Caccaki ‘Yan Fanshon Jahar Kano
Kakakin darikar Kwankwasiyya ya caccaki yan fanshon jahar Kano.
Ya ce basu da godiyar Allah duk da abinda Rabiu Kwankwaso yayi musu.
Yan fansho sun kai karar Kwankwaso ofishin hukumar EFCC.
Kano – Dan takarar kujerar mataimakin gwamnan Kano a zaben 2019 karkashin jam’iyyar People Democratic Party (PDP), Aminu AbdulSalam, ya caccaki yan fanshon dake zagin maigidansa, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.
Aminu AbdulSalam wanda shine Kakakin darikar Kwankwasiyya yace duk dan fanshon da ya zagi Kwankwado zai shiga wuta saboda marasa godiya ne.
Read Also:
Yace yan fanshon basu kyauta ba yayinda suka kai karar Kwankwaso wajen hukumar EFCC kan zargin yayi amfani da kudin fansho.
Aminu yayi magana a daren Alhamis a wani shirin gidan rediyon Express kan gayyatar da EFCC ta yiwa Kwankwaso kan zargin almundahana da karkatar da kudin al’umma da kuma baiwa abokansa gidaje, PremiumTimes ta jiyo.
Aminu AbdulSalam yace Kwankwaso ne ya karawa yan fansho kudi zuwa N5000 saboda haka duk dan fanshon da bai godewa hakan ba wuta zai shiga.
A cewarsa:
“Kwankwaso yayi iyakan kokarinsa wa yan fashi kuma duk dan fanshon da bai gode da abinda Kwankwaso yayi ba zai shiga wuta.”
Za ku tuna cewa 2015, yan fanshi sun kai karar Kwankwaso wajen hukumar EFCC kan zargin karkatar da kudin fansho.