Yadda Karnuka Goma Suka Afka wa Yaro a Jahar Anambra

 

Wasu karnuka goma sun afka wa wani yaro ɗan shekara biyu tare da cinye shi a wata makaranta mai zaman kanta a garin Amokpo Umuanunwa a jahar Anambra.

Jaridar The Nation a Najeriya ta rawaito cewa iyayen yaron sun je da shi makarantar ne don yi masa rajistar fara makaranta lokacin da lamarin ya faru.

Rahotanni sun nuna cewa mai makarantar, mai suna Chinedu Oka, na kiwon karnunka ne a harabar makarantar duk da gargain da aka yi masa a garin, kan haramta kiwon karnuka.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewa iyayen karamin yaron na cike takardun yin masa rajistar fara makaranta ne lokacin da yaron ya sulale zuwa inda karnukan suka far masa.

“Karnukan su goma ne kuma nan da nan suka auka wa yaron suka yi yaga-yaga da shi kuma da yake babu kowa a kusa da wurin bare a ceto shi,” cewarsa.

An rawaito cewa nan take wasu samari suka shiga harabar makarantar suka harbe duka karnukan, yayin da iyaye da dama suka cire ‘ya’yansu daga makarantar nan da nan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here