Mutane 2 Sun Rasa Ransu Sanadiyyar Tashin Bom a Birnin Jalalabad na Afghanistan

 

Bom ya kashe mutum biyu a birnin Jalalabad na Afghanistan

Wani abin fashewa da aka sa a bakin titi a birnin Jalalabad na Afghanistan ya kashe a ƙalla mutum biyu tare da jikkata wasu da dama.

Hukumomi a birnin sun ce harin ya yi yunƙurin auka wa motocin Taliban ne.

A baya, an yi wani harin a Kabul, babban birnin Afghanistan inda mutum biyu suka samu raunuka.

Babu wata ƙungiya da ta ɗau alhakin kai hare-haren.

Akwai masaniyar cewa mayaƙan ƙungiyar IS na kaddamar da ayyukansu a yankin Jalalabad.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here