Rabiu Kwankwaso Zai Hadu da Gwamna Wike
‘Dan takarar jam’iyyar hamayya ta NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso zai yi zama da Nyesom Wike.
Da alama Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana neman wanda zai zama abokin takararsa a 2023.
Haduwar Kwankwaso za ta zo ne sa’anni kadan bayan Peter Obi ya gana da Gwamnan a gidansa.
Rivers – Mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso zai hadu Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto na musamman cewa Rabiu Musa Kwankwaso yana shirin sa labule da jagoran na jam’iyyar PDP.
‘Dan takaran shugaban kasar zai gana da Gwamnan ne a lokacin da yake neman wanda zai yi masa takarar mataimakin shugabancin kasa.
A halin yanzu Sanata Kwankwaso da jam’iyyarsa ta NNPP su na tsakiyar tattaunawa da ‘dan takarar jam’iyyar LP watau Mista Peter Obi.
Read Also:
An samu tasgaro a tattaunawar yayin da kowane bangare ya dage a kan cewa shi za a ba tikitin shugaban kasa idan jam’iyyun sun hade.
Rahoton ya ce watakila tsohon Gwamnan na Kano zai zauna da Wike ne domin neman wata mafitar idan har ya gaza shawo kan Obi.
Za a gana da Fatakwal
Hadiman Kwankwaso sun tabbatar da cewa da kimanin karfe 2:30 na ranar Juma’a, 24 ga watan Yuni 2022 za ayi wannan zama a Fatakwal.
Legit.ng za ta tuna, gabanin ficewar ‘dan takaran na NNPP daga PDP, Mai girma Wike ya hadu da shi a gidansa da ke birnin tarayya Abuja.
Ko bayan banban ‘dan siyasar na Arewacin Najeriya ya sauya-sheka zuwa NNPP, dangantakarsa da Gwamnan na jihar Ribas ba ta cabe ba.
‘Ya ‘yan jam’iyyar hamayya ta PDP na reshen jihar Kano duk sun zabi Wike ne a lokacin zaben fitar da gwanin zama shugaban kasa a PDP.
Har yanzu NNPP ba ta tsaida takamaimen ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa ba, babu mamamki Wike yana cikin lissafin da ake yi.