Legas: Gwamnan ya Fusata da Rikicin Kabilanci, ya yi Tsokaci Mai Zafi
Gwamnan jihar Legas, Sanwo-Olu, ya kai ziyara Fagba da ke wurin Ifako-Ijaiye, don jajanta wa wadanda asara ta hau kansu sakamakon wani rikici
Rikicin ya barke tsakanin Hausawa da Yarabawa mazauna yankin, wanda ya ja asarar dukiyoyi masu yawa – Gwamnan ya lashi takobin hukunta duk wanda ya gano yana da hannu a fadan, kuma zai yi kokarin biyan duk asarorin da aka tafka Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya yi takaicin faruwar wani rikici da ya barke tsakanin Yarabawa da Hausawa a Fagba, wuraren Ifako-Ijaiye da ke jihar.
Read Also:
Bayan Sanwo-Olu ya kai ziyara wuraren ne a ranar Talata, ya lashi takobin hukunta duk wadanda ya gano suna da hannu a cikin rigimar, The Punch ta wallafa. Ya tabbatar wa da mazauna wurin, wadanda rikicin ya shafa cewa zai share hawayensu.
Gwamnan da ya samu rakon mataimakinsa, Dr Obafemi Hamzat, sakataren gwamnatin jihar, Folasade Jaji, mai bai wa gwamnan shawara a harkar ilimi, Tokumbo Wahab da shugaban ma’aikata, Hakeem Muri-Okunola.
A cewarsa, “Irin asarar da na gani a wurin nan ta kazanta. Don haka za mu fara bincike take-yanke, a kan lamarin. Shugabannin unguwannin za su zauna su rubuta sunayen wadanda aka barnatar wa da dukiya. “Muna so mu yi amfani da wannan damar wurin fadakar da bata-gari da ke kusa, don sannu a hankali za mu gano su.
“Idan mutum ya san bashi da wani aikin yi ko kuma yana cikin wadanda suka assasa rikicinnan, wannan ne jan kunne na karshe.” Ya kara da cewa, “Gwamnati za ta yi bakin kokarinta wurin biyan asarar, kuma masu shaguna su ji tsoron Allah yayin rubuta asarorinsu.”