Sunayen Manyan ‘Yan Siyasar da ake Tunanin Tinubu zai ba Ministoci

 

 

Wani rahoto da jaridar Nigerian Tribune ta wallafa na nuni da cewa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fara duba tsarin majalisar ministocinsa da kuma ta masu kula da tattalin arziƙi.

Za a rantsar da Tinubu ne dai a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16.

A rahoton wanda jaridar ta fitar ranar Laraba, 17 ga watan Mayu, ta bayyana cewa wata majiya ta shaida ma ta cewa, zaɓaɓɓen shugaban kasar na son mayar da hankali sosai wajen zaɓo mutanen da suka dace da za su taimaka masa wajen cimma duka manufofinsa.

Tinubu na son bai wa mara ɗa kunya

Majiyar ta bayyana cewa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya san cewa mutane sun sanya tsammani sosai a kan gwamnatinsa, kuma ya san irin gajen haƙurin ‘yan Najeriya.

A dalilin haka ba ya so a samu matsala kan manufofin nasa, don haka nema yake son ya zamto ya gama zaɓar mutanen da za su yi aiki tare kafin 29 ga Mayu.

Kamar dai yadda majiyar wacce ba a bayyana sunanta ba ta bayyana, waɗannan su ne sunayen manyan ‘yan siyasar da ake tunanin Tinubu zai ba ministoci, da kuma ma’aikatun da za a tura su:

1. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje (Kano) – Ministan harkokin noma da raya yankunan karkara

2. Gwamna Nyesom Wike (Ribas) – Ministan harkokin cikin gida

3. Dakta Kayode Fayemi – Ministan harkokin ƙasashen waje

4. Farfesa Peter Okebukola – Ministan Ilimi

5. Malam Nuhu Ribadu – Ministan harkokin ‘yan sanda

6. Sanata Aisha Binani – Ministar wutar

7. Babatunde Ogala – Ministan shari’a

8. Wale Edun – Ministan kuɗi, kasafi da tsare-tsare

9. M*ofo Boyo – Ministan mai

10. Ayo Abina – Ƙaramin ministan tsare-tsare

11. Femi Gbajabiamila – Shugaban ma’aikata

12. Yewande Sadiku – Ministan masana’antu

13. Farfesa Yemi

14. Oke Iyin

15. Aboyeji Dayo

16. Israel Uju Ohanenye

Sai dai jaridar The Guardian ta wallafa cewa akwai wasu daga cikin ministocin gwamnatin Buhari da suka aika kokon bararsu zuwa ga Tinubu.

Ta ce wasunsu tun kan ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa Faransa suka rika aika masa da sakonni na neman a sanyasu cikin wadanda za a yi tafiyar da su.

Tanadin da Tinubu ya yi wa waɗanda ba za su samu muƙaman ministocin ba

Bugu da ƙari, majiyar ta bayyana cewa, akwai yiwuwar a sanya waɗanda ba su sami muƙamin ministan ba cikin hukumar masu kula da tattalin arziki.

Haka nan kuma, akwai yiwuwar a bai wasu daga cikinsu shugabantar wasu hukumomin da ke samar da kuɗaɗen shiga.

Akwai yiwuwar bai wa ‘yan adawa muƙamai

A cewar majiyar, Tinubu na son bayar da muƙaman ministocin da sauran muhimman muƙamai ga ‘yan jam’iyyar APC ne kawai.

Sai dai a shirye kuma ya ke ya yi bai wa wasu hazikai daga wajen jam’iyyar waɗanda ya ke ganin za su taimaka masa wajen cimma burinsa na farfado da tattalin arzikin kasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here