Matar Aure ta yi Hayar Macen da Za ta Dinga Gamsar da Mijinta Akan N145k 

 

Wata matar aure tayi abun mamaki na daukowa mijinta hayar macen da za ta dunga gyara masa shimfida.

Patheema ta ce ba za ta iya gamsar da mijin nata ba a bangaren kwanciyar aure don haka ta samo wacce za ta taimaka mata.

Ta samu wacce ta nuna sha’awar wannan aiki bayan ta tallata shi a yanar gizo, kuma za a dunga biyanta albashi duk wata.

Wata mata tayi hayar wacce za ta taimaka mata wajen biyawa mijinta bukata ta bangaren kwanciyar aure bayan ta tallata aikin a yanar gizo. Matar mai shekaru is 44 mai suna Patheema daga kasar Thailand, ta je shafin Tiktok ta tallata aikin mai ban al’ajabi.

Ta yi bayani yayin tallata aikin cewa tana son daukarwa mijinta hayar sa-‘daka domin ta yarda cewa bata gamsar da shi a gado, shafin LIB ya rahoto.

Matar ta bayyana a bidiyon cewa:

“Ina son daukarwa mijina hayar sa-‘daka guda uku.”

Ta kuma jaddada a bidiyon cewa dole matan su kasance tsakanin shekaru 30-35 kuma ya zamana sun kammala kwaleji ko suna da digiri.

Matar ta kuma bayyana cewa dole sa-’dakar ta kasance da takardar gwajin lafiya don tabbatar da basa dauke da cutar kanjamau.

Bidiyon tallan ya ci gaba da cewa:

“Za a biya ta akalla £340 (N145k a kudin Najeriya) duk wata, za a baku wajen kwana da abinci kyauta. Amma ya zama dole ku taimaka mun. Mutum biyu za su dunga taimakamun da aiki kan takardu a ofishina, sannan mutum daya za ta kula da mijina da yarana.”

Matar ta kuma ba wadanda za su nemi aikin tabbacin cewa ba za ta raina mai debewa mijin nata kewa ba.

“Ina mai ba da tabbacin cewa fada ba zai shiga tsakaninki da ni ba. Zan bari mijina ya zabi da wacce yake so ya kwanta ko yake so tsaya da ita. Ba raba lokaci, zai iya zaba da kansa,” in ji ta.

Duk da abun al’ajabin da ke tattare da wannan aikin, ma’auratan sun samu wacce ke sha’awar aikin kuma sun karbeta hannu bibbiyu a gidansu.
An tattaro cewa Patheema ta bukaci wata kyakkyawar mata mai shekaru 33 da ta shigo cikin ahlinta a matsayin sa-‘dakar mijinta.

Ta kuma ce koda dai ba macen da mijinta ya yi tsammanin samu bane, ya yarda ta zama ‘karamar matarsa’, kuma Pattheema ta rufe daukar aikin.

Matar ta kasance aminiyar Patheema kuma su dukka ukun sun ce suna shirin kula da junansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here