Manyan Dalilai 9 da Yasa Mulkin Tinubu ya fi na Buhari – Reno Omokri
FCT, Abuja – Hadimin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya kwatanta mulkin Buhari da na Shugaba Tinubu.
Omokri wanda mai fashin baki ne a harkar siyasa ya jero dalilai 9 da ke nuna mulkin Tinubu ya fi na Buhari.
Mutane da dama na yawan kwatanta gwamnatin Buhari da na Tinubu don sanin wane ya fi dama-dama a tsakani.
1. Tattalin arziki
Omokri ya ce Najeriya ta fuskanci matsalar tattalin arziki na tsawon shekaru 20 yayin da matsalar ta karu bayan hawan Buhari.
Sai dai Omori ya ce an samu bunkasar tattalin arziki tun bayan hawan Tinubu saboda tsarte-tsarensa.
2. Kasuwancin masu hannun jari
Omokri ya ce a lokacin Buhari an samu matsala a bangaren zuba hannun jari yayin da a gwamnatin Tinubu kuwa aka samu ci gaba.
3. Kasuwar ‘yan canji
Mai fashin bakin ya ce a mulkin Buhari, Bankin CBN ya na kashe dala biliyan 1.5 a ko wace wata don kokarin kare darajar naira.
Ya ce an samu sabanin haka a mulkin Tinubu yayin da ya kawo sabbin tsare-tsare a hada-hadar canji.
4. Yaki da cin hanci
Har ila yau, Omokri ya ce an samu badakalar makudan kudade a wurin Ministocin Buhari yayin da a mulkin Tinubu ya ke daukar matakin dakatar da su tare da fara bincike.
5. Sauyi a shige da ficen kasar
Read Also:
Ya bambance tsakanin mulkin Buhari da Tinubu yayin da ya ce ana samun matsalar samun Fasfo a mulkin Buhari.
Ya ce a yanzu Tinubu ya kawo tsarin bayar da Fasfo din cikin kankanin lokaci ta yanar gizo.
6. Tsare-tsaren Kirifto
A bangaren Kirifto, Omokri ya ce:
“Gwamnatin Buhari ta dakatar da harkokin Kirifto a kasar wanda ya jawo asarar dala tiriliyan 1.8 ga ‘yan Najeriya.
“Tinubu ya dawo da martabar Kirifto inda ya janye dakatarwar wanda hakan ya bai wa matasan Najeriya damar samun kudaden shiga.”
7. Gudanar da iyaka
Gwamnatin Buhari ta rufe iyaka inda ta sanya doka kan shigo da wasu kayayyaki da ya jawo tsadar kaya a kasar.
Omokri ya yabawa Tinubu inda ya ke daukar matakai don ganin ya kawo sauyi a bangaren da ya shafi iyakar kasar.
8. Wadatar man fetur
An sha samun matsalar karancin man fetur a lokacin mulkin Buhari a lokuta da dama musamman a karshen shekara.
Omokri ya ce sabanin haka aka samu a mulkin Tinubu yayin da aka fara inganta matatun mai a kasar tare da na Dangote.
9. Harkar tsaro
A lokacin mulkin Buhari, sojoji sun shiga Zaria inda suka hallaka mutane 248 mafi yawanci ‘yan Shi’a amma babu wanda aka hukunta.
Amma ya ce Tinubu na kokarin daukar mataki a duk lokacin da wani soja ya ci zarafin farar hula musamman abin da ya faru a Rivers.
Ya kara da cewa a zamanin Buhari ‘yan bindiga sun hana mutane sakat kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, amma a yanzu zaka yi tafiya hankali a kwance.