‘Yan Daba Sun Kai Farmaki Kan Motar Kamfen ɗin Mataimakin Gwamnan Jihar Edo

 

Wasu maharan sun yi kaca-kaca da motar kamfen mataimakin gwamnan jihar Edo kuma ɗan takarar gwamna a PDP, Philip Shaibu.

Kodinetan kamfen Shaibu ya bayyana cewa lamarin ya auku ne jim kaɗan bayan sun gama taro a Ekpoma.

Tuni dai rundunar ƴan sanda ta kwato motar da maharan suka lalata kuma sun fara bincike kan abin da ya faru.

Jihar Edo – Wasu ‘yan daba ne sun lalata motar kamfen mataimakin gwamnan jihar Edo kuma dan takarar gwamna, Philip Shaibu a Ekpoma, karamar hukumar Esan ta Yamma.

Rahotan jaridar Leadership ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadi bayan wani taro da magoya bayan Shaibu suka yi a garin Illeh da ke gunduma ta 10.

Jihar Edo – Wasu ‘yan daba ne sun lalata motar kamfen mataimakin gwamnan jihar Edo kuma dan takarar gwamna, Philip Shaibu a Ekpoma, karamar hukumar Esan ta Yamma.

Rahotan jaridar Leadership ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadi bayan wani taro da magoya bayan Shaibu suka yi a garin Illeh da ke gunduma ta 10.

Da yake bayyana abin da ya faru ta wayar tarho, Kodinetan yakin neman zaben Shaibu a yankin, Otoide Abas ya ce ‘yan sanda sun dauko motar da maharan suka lalata.

Yan sanda sun shiga lamarin

A cewarsa, yanzu haka motar na hannu ƴan sanda a caji ofis ɗin da ke yankin.

A kalamansa, kodinetan kamfen Shaibu ya ce:

“Mun kammala wani taro da mambobin jam’iyyar PDP na Ward 10 (Illeh) lokacin da lamarin ya faru. Mun fara taron ne da misalin karfe 5:00 na yamma kuma muka ƙarƙare shida saura kaɗan.

“Bayan taron, sai muka shiga motar Bas Sienna da Shaibu ya ba mu zuwa Ekpoma don ganawa da sauran magoya bayanmu, mun ɗan tsaya a wata ƙaramar kasuwa a Ekpoma don sayan Suya.

“Muna tsaye a wurin da zamu yi siyayya sai muka ga wasu yara maza kusan bakwai sun sauko daga wata motar bas da ke kusa, suka fara harbi, duk muka gudu domin tsira, sai suka je inda muka ajiye motar suka lalata ta.”

“‘Yan sanda sun ɗauko motar a wannan dare kuma a yanzu da nake magana da ku, ina ofishin ‘yan sanda ne saboda an ce in kawo kaina yau (Litinin).”

A watan Nuwamba, Shaibu ya ayyana shiga tseren takarar gwamna a inuwar jam’iyyar PDP, zai fafata a zaben fidda gwanin jam’iyya, kamar yadda Daily Post ta tattaro.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com