Ba Hakanan Kawai Shugaba Buhari ya Nada ni Ministan Wutar Lantarki ba – Abubakar Aliyu

 

Abubakar Aliyu, sabon ministan wutar Lantarki ya ce ba hakanan kawai Shugaba Buhari ya nada shi ministan Wutar Lantarki ba.

Aliyu ya bayyana cewa shugaban kasar ya nada shi ministan ne domin ya tafi ya tabbatar komai ya tafi dai-dai a ma’aikatar kuma an ci nasara.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa da ya yi a lokacin da ya ke ganawa da direktoci da ma’aikatan ma’aikatar na wutar Lantarki.

FCT, Abuja -Sabon Ministan wutar lantarki, Injiniya Abubakar Aliyu, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya tura shi ya karbi ragamar shugabanci a ma’aikatar ne saboda wani dalili na musamman, Daily Trust ta rawaito.

Daily Trust ta rawaito cewa Aliyu ya bayyana hakan ne yayin da ya kama aiki a Ma’aikatar Wutar Lantarki a Abuja a ranar Litinin.

Da ya ke yi wa direktoci da ma’aikatan ma’aikatar jawabi, ya ce:

“Na san kun yi aiki sosai, Na zo nan ne domin in taimaka muku, ko da ba ku ko babu ku domin abin da aka turo ni in tabbatar shine mu yi nasara.

Wanda ya dauke ni aiki ya turo ni nan ne saboda wani dalili.” Da ya ke bayyana dalilin, Sabon Ministan Wutar Lantarki ya ce an turo shi ne domin ya tabbatar an yi komai yadda ya dace a bangaren wutar lantarki.

Aliyu ya kuma nemi hadin kan masu ruwa da tsaki yana cewa;

“Ba hanayenku kadai na ke so ba wurin aiki har da zuciyarku. nan ne gaskiya da jajircewa ya ke.

“Aikin mu zai taba rayukan dukkan yan Nigeria don haka a zo nan ne domin in kara wa aikin ku inganci.”

Ministan yayin da ya ke neman goyon bayan jami’an ma’aikatan ya ce ya saurari mukaman jami’an amma yana bukatar hakan ya zama aiki.

Martanin sakataren dindindin na ma’aikatar wutar lantarki

Sakataren dindindin na ma’aikatar, Mr Williams Alo ya ce jami’an a shirye suka su bawa ministan goyon bayan da ya ke bukata.

Alo ya ce:

“Mun san ka zo nan ne domin ka cigaba da aiki mai kyau na shugaban kasa da ya shafi sashin wutar lantarki. Muna tabbatar da maka cewa za mu mayar da hankali don yin ayyukan mu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here