Gwamnatin Nasarawa ta Haramta Amfani da Sayar da Gawayi a Jahar ta
Gwamnatin Jahar Nasarawa a Najeriya ta haramta amfani da sayar da gawayi da kuma amfani da shi a wani yunƙuri na kare muhallin jahar.
Read Also:
Jaridar Punch ta rawaito babban sakataren ma’aikatar kula da muhalli na jahar Aliyu Agwai inda ya ce hanyoyin da ake bi wajen samar da gawayi na da illa matuƙa ga muhalli ta hanayar jawo ɗumamar yanayi.
Babban sakataren ya bayyana haka ne a yayin wani jawabi ga manema labarai a ranar Asabar.
Ya bayyana cewa sare itatuwa zai cutar da wasu dabbobi sakamakon za su rasa wuraren zama wanda hakan zai iya illa ga muhalli.
Ya kuma yi gargaɗi ga masu sayar da gawayin da kuma amfani da shi da su bari ko kuma a kama su.