Shugaban (NITDA) ya Halarci Taron ba wa Ministan Sufuri Ɗan Amanar Daura

Mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), a jiya, ya halarci taron bikin naɗin ministan sufuri, mista Rotimi Chibuke Ameachi a matsayin ɗan Amanar Daura, tare da halartar liyafar taya shi murna.

Bikin naɗin sarautar wanda aka gudanar a birnin Daura na Jihar Katsina, ya samu halartar manyan muhimman mutane daga sassa daban-daban na Nageriya, daga ciki akwai:

Mai girma mataimakin gwamnan Jihar Kano, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, jigo a jam’iyyar APC, Onarabul Faruƙ Adamu Aliyu Birnin Kudu, tsohon shugaban dakarun sojin ƙasa, Laftanar, Janar Yusuf Buratai, mai girma Ɗan Amanar Dutse, kana kuma ƙusa a jam’iyyar APC, Alhaji Nasiru Dano, mai girma ɗan majalissar dakoki na Jihar Jigawa, Onarabul Abubakar Sadik Jallo, da sauran muhimman mutane da dama.

Lahadi, 6 ga watan Janairu, 2022.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here