Gwamnan Ondo ya yi wa Gwamnatin Tarayya Martani Kan Siyan Makamai ga Rundunar Amotekun

 

Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya sanarwa gwamnatin tarayya cewa makaman da zai bai wa Amotekun ne don kariya ga jama’a.

Ya sanar da cewa rantsuwa kowanne gwamna ya dauka na bai wa jama’ar jiharsa kariya, don haka ba zai ci amana ba.

Ya jaddada cewa, dalilan da Garba Shehu ya fadi daga fadar shugaban kasa ba su cika gamsassu ba da zasu hana shi mika makaman ba.

Ondo – Gwamnan jihar Ondo Oluwarotimi Akeredolu yayi wa gwamnatin tarayya martani cewa nufinsa na siyan makamai ga rundunar Amotekun shine don bai wa jama’ar Ondo kariya.

Akeredolu ya bayyana cewa dalilan da hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya bayar na ci gaba da kin amincewa da amfani da nagartattun makamai da jami’an tsaron jiharsa, ba su da ma’ana a yayin da ake fuskantar kalubalen tsaro a jiharsa

The Nation ta rahoto, Gwamnan Ondo ya ce gwamnatin jihar Katsina ba ta musanta furucinsa na amfani da AK47 ba da ‘yan bangansu ke yi ba a lokacin horo.

Akeredolu ya tsaya kan cewa dole ne jami’an tsaron Amotekun da ke da goyon bayan doka a kowane yanki na kasar nan su samu damar mallakar makamai kamar yadda masu laifi ke yi.

Ya bayyana cewa, a kula da kiran da kungiyar ‘yan sandan jihar ta yi, kuma a yi amfani da sauyi a inda ya cancanta.

A cewarsa:

“Kowane Gwamna ya rantse kan cewa zai kare jiharsa da jama’a. Dole ne a bar jiharsa ta sanya jami’an tsaro a matsayin rundunonin daidaitawa don tunkarar miyagun ‘yan ta’addan.

“Lokaci ya yi da za mu tunkari wadannan ‘yan ta’adda tare da dawo da kwarin gwiwar jama’a. Ba za mu iya yin abu ɗaya akai-akai ba kuma muna tsammanin sakamako daban-daban.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here