Sarkin Musulmai, Sa’ad Abubakar ya Bukaci Shugaba Buhari ya Dau Mataki Kan Sauya kudi

 

Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya dauki matakan gaggawa na shawo kan wahalar da jama’a ke ciki a sanadiyyar sauyin kudi domin kauce wa bore.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Sultan din ya nuna takaicinsa a jiya Litinin kan lamarin inda ya nuna damuwa kan yadda jama’a suka fada cikin yanayi na yunwa da bacin rai saboda canjin kudin.

Matsalar sauyin kudin ta kara tsananta a tsakanin jama’a bayan da rahotanni suka nuna cewa bakuna sun daina ansar tsoffin takardun kudin na naira 200 da 500 da kuma 1,000.

A ranar Laraba da ta gabata ne Kotun Kolin kasar ta hana Babban bankin kasar aiwatar da tsarinsa na hana amfani da tsofaffin kudin a ranar 10 ga watan nan na Fabarairu, har sai ta yanke hukunci a kasar da gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka shigar a kan lamarin.

A gobe Laraba ne Kotun Kolin ta ce za ta yanke hukunci a kan karar wadda gwamnonin jihohin uku suka shigar.

Jihohin Kano da Naija da Ekiti da kuma Ondo suma sun bi sahun jihohin uku inda suka shigar da kara a gaban kotun kolin kan batun sauyin kudin.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here