Manyan ‘Yan Siyasa 5 da Suka Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP
Gabannin babban zaben 2023, manyan yan siyasa a jam’iyyun All Progressives Congress (APC) mai mulki da Peoples Democratic Party (PDP) mai adawa sun fara sauye-sauyen sheka domin kare kudirin siyasarsu.
A yan kwanakin nan da suka gabata, jam’iyyar APC mai mulki ta rasa wasu manyan mambobinta zuwa PDP. Ga manyan jiga-jigan APC da suka koma PDP gabannin babban zaben kasar mai zuwa.
1. Ahmed Babba Kaita
Ahmed Babba Kaita, sanata mai wakiltan Katsina ta arewa, yankin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sauya sheka daga APC zuwa PDP a ranar Laraba, 20 ga watan Afrilu.
A wata sanarwa daga hadimin labaransa, Abdulkadir Lawal, Babba-Kaita ya ce ya sauya sheka ne saboda yadda gwamnan jihar, Bello Masari ya yi babakere ya hana ruwa gudu a harkar jam’iyyar a jihar.
Ya kuma bayyana cewa PDP na wakiltan ra’ayinsa.
2. Mogaji Joseph Tegbe
Hakazalika, tsohon dan takarar gwamna karkashin APC a jihar Oyo, Mogaji Joseph Tegbe, ya sauya sheka zuwa PDP.
Read Also:
Hakan ya faru ne saboda yawan rikice-rikice a APC wanda ya ki ci ya ki cinyewa.
An sanar da batun sauya shekar Tegbe ne a daren ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, ban tsawon watanni yana fuskantar matsin lamba.
3. Aminu Muhammad Achida
Kakakin majalisar dokokin jihar Sokoto, Aminu Muhammad Achida, ya bar APC zuwa PDP.
Achida ya gabatar da wasikar sauya sheka ga majalisar dokokin a lokacin zamanta na ranar Alhamis, 14 ga watan Afrilu.
4. Murtala Bello Maigona
Murtala Bello Maigona, dan majalisar dokokin jihar Sokoto mai wakiltan mazabar Wammako 2, ya zama dan PDP a yanzu.
An sanar da sauya shekarsa daga APC tare da na kakakin majalisar, Achida.
5. Abubakar Sulaiman
Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Sulaiman ma ya koma PDP.
An zabe shi a matsayin dan majalisa mai wakiltan mazabar Ningi a 2019 a karkashin inuwar jam’iyyar APC.
Sulaiman wanda ya kuma kasance shugaban kungiyar yan majalisun jiha na Najeriya, ya sanar da batun sauya shekarsa a lokacin buda bakin Ramadana wanda Gwamna Bala Mohammed ya shirya, wanda aka yi a gidan gwamnatin jihar Bauchi a daren Asabar, 16 ga watan Afrilu.